'Yan Demokrat Sun Bayyana Takaicinsu Kan Umurnin Trump

Fadar White House ta ba wasu jami'ai umurni, kamar tsohon mai bada shawara Don McGahn, akan kada su sake su amsa tambayoyi daga kwamitin shari'a na majalisar wakilan Amurka.

Kwamitin shari'a na majalisar wakilan Amurka zai jefa kuri'a a yau Alhamis, akan ko ya bada umurnin kiran bada bahasi, ga jami’an da suka yiwa Trump yakin neman zabe na yanzu da na baya ko a’a.

A zaman wani bangaren binciken da ake yi akan ko an nemi hana doka ta yi aikin ta, da batun rashawa da kuma batun manufofin gwamnatin kasar akan raba iyalai, da tsare yara a wasu cibiyoyi dake bakin iyakar kasar da Mexico.

'Yan jam’iyyar Democrat, da suka jagoranci kwamitin sun bayyana takaicinsu, akan abinda suka kira rashin samun hadin kai daga fadar White House, da kuma ma’aikatun gwamnatin tarayyar kasar akan bukatar da suka gabatar ta neman yiwa jami’ai tambayoyi da kuma samun wasu takardu.

Fadar White House ta ba wasu jami'ai umurni, kamar tsohon mai bada shawara Don McGahn, akan kada su sake su amsa tambayoyi daga kwamitin, a yayin da 'yan jam'iyyar Republican, ke zargin ‘yan Democrat da jan binciken da ake yi da kuma bata lokacin 'yan majalisar.