'Yan Gudun Hijira Na Zanga-Zanga a Agadaz

'Yan Gudun Hijira Na Zanga-Zanga A Agadaz

An shiga yini na uku da dumbin 'yan gudun hijira daga kasashen Chadi, Sudan da Afirka ta Tsakiya suke zanga zanga a ofishin UNHCR mai kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Agadez a Jamhuriyar Nijar.

Akalla 'yan gudun hijira 2,400 ke zaune a ciki wannan sansani, daya daga cikinsu kuma sun yi tattaki zuwa ofishin na UNHCR inda suke zaman dirshan dauke da kwalayen da suka rubuta matsalolinsu a kai

'Yan gudun hijirar na korafi ne kan rashin cika alkawari da hukumomi suka yi, sun kuma ce rayuwa ba dadi a Nigar, suna zaune ba ilimi, kula da kiwon lafiya, ba kuma aikin yi.

Wakilin UNHCR, Mahamat Nur Abdulaye, ya ce, a lokacin da 'yan gudun hijirar suka zo ofishin na su, sun zauna da su suka tattauna, inda suka shaida masu ba su da hurumin mayar da su inda suka fito.

Shi kuwa shugaban da'irar Agadez Docta Maman Bukari jan hankali ya yi masu na su yi hakuri su bi hanyoyin da ya dace a magance matsalar.

Saurari cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Gudun Hijira Na Zanga-Zanga a Agadaz