'Yan Jarida A Plato Sun Sha Alwashin Bada Gudummuwa Ga Nasarar Zabe

Tambarin Hukumar Zaben Najeriya

‘Yan jarida a jahar pilato sun tunatar da kansu kan muhimmancin gabatar da rahotanni da zasu hana tada husuma a lokaci zabubbuka da za’a gudanar a Najeriya.

A wani taron kara wa juna sani da cibiyar sasantawa ta Humanitarian Dialogue ta shirya wa wakilan kafafen yada labarai daban-daban a jahar pilato, gabanin manyan zabubbuka dake karatowa a Najeriya, ‘yan jaridar sun ci alwashin gudanar da aikinsu bisa kundin tsarin aikin.

Jami’in cibiyar Humanitarian Dialogue, Ibrahim Sale Hassan yace sun shirya taron bitar wa ‘yan jaridan ne ganin yadda suke da muhimmaci wajen gudanar da zabe cikin tsanaki.

Jimi’in dake wayar da kan jama’a a hukumar zabe ta kasa dake jahar Pilato, Osaretin Imahiyereobo yayi amfani da dammar wajen shaida wa wadanda keda katunan zabe fiye da guda daya cewa ba zasu iya kada kuri’a ba.

Taron bitar mai taken gudunmowar ‘yan jarida wajen gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba, ya kuma tattauna kan gudunmuwan sauran masu ruwa da tsaki a harkar zabe zasu bayar wajen yin zabe ba tare da an kashe kowa ko lalata dukiya ba.

Saurari rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Bita kan aikin jarida-3:30"