'Yan Kabilan Jukun a Kudancin Najeriya Sun Koka

Mutane a jihar Taraba.

An ganmo wannan bashi da nasaba da addini ko kabilanci illa siyasa
‘Yan kabilan Jukun dake kudancin Najeriya sun koka akan yanda suka ce ana kashe mutanen su masamman a jihar Taraba, kuma suka ce sun ganmo wannan bashi da nasaba da addini ko kabilanci illa siyasa.

Shugaban kabilan Jukunawa mazauna kudancin Najeriya, Mr. Banjamin Bako, yace daga lokacin da aka fara wannan rikicin kawo yanzu kauyuka kusan hamsin suka rasa matsuguninsu sannan mutane fiye da dubu biyu ne suka rasa rayukansu.

Mr. Bako, yace danme wannan lamarin sai a yankin kudancin Taraba ne ake ta rikici da yaki karewa, kuma abun ya koma tsakanin su kansu ‘yan kabilan Jukun Musulmi da mabiya addinin krista.

Yace a bisa binciken da sukayi sun gano cewa ‘yan siyasa ne ke hadasa wannan, domin yace suna kallo amma sun yi shuru babu wani zababe da ya fito ya soki wannan lamarin.

Shi kuwa wani dan majalisar dokokin jihar Mr. Daniel Ishaya Gani, cewa yayi rokon Allah suke yi akan wannan musibar da ya afkamasu.

Ya kuma kara da cewa mulki Allah ne ke badawa, duk dan siyasan da ya dauka cewa zai hadasa fitina domin biyan bukatarsa,yace wannan yana yiwa kasan illa ne.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Kabilan Jukun a Kudancin Najeriya Sun Koka - 2'35"