Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tafka Asarar Rayuka da ta Dukiyoyi a Rikicin Wukari


Sojojin kwantar da tarzoma na kokarin kashe wutar rikici a Wukari, jahar Taraba.

Baicin kona gidaje,akwai kuma matsalar rashin abinci inji wani dan garin da yayi kira a kafa mu su sansanonin zama

Shaidun gani da ido sunce a kalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu a rigingimun kabilancin da suka barke a karshen wannan mako a garin Wukari, jahar Taraba. Yayin da hankula ke neman kwantawa, yanzu haka dubban jama’a na cikin wani mawuyacin hali na rashin matsuguni da kuma abinci, inda ake tsoron barkewar cututtuka. A rahoton da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya aiko wani dan garin yayi bayani kamar haka:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG