'Yan Kasuwa Sun Koka Kan Shirin Karin Kudin Shiga Jirgin Sama a Najeriya

Ma’aikatar sufurin jiragen sama da hukumar FAAN sun fara gwaji a kan aikin sufurin jiragen saman Najeriya yayin da ake sa ran bude filayen jiragen saman kasar kwanan nan.

Gabanin sake bude ayyukan sufurin jiragen saman Najeriya, Ministan Sufurin kasar Honarabul Hadi Sirika, ya bukaci fasinjojin kasar su zamo masu bin ka’idojin da hukumomin lafiya suka gindaya saboda kare lafiyarsu duk da cewa gwamnatin kasar ta shigo da wasu sabbin na’urori da za su taimaka wajen takaita cudanya, a daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da fuskantar barazana sakamakon annobar coronavirus.

Ministan ya kuma bayyana gamsuwa da wani gwajin aikin jiragen sama da suka gudanar a ranar Asabar 27 ga watan Yuni, na na’urori da sauran kayayyakin kare kai da na yin gwajin zafin jiki.

Bayan da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama wato FAAN ta sanar da shirin karin kudin tikitin shiga jirgin sama da kashi 100, ‘yan kasuwa irinsu Muhammad Auwal Mu’azu sun tofa albarkacin bakinsu a kan yadda wannan karin zai shafi kasuwancinsu, zai kuma iya janyo tsadar kayayyaki musamman a yanayin da ake ciki na annobar cutar COVID-19.

Dr. Hamid Muhammad, Malami a jami'ar Binuwai wanda ya sauka a filin jiragen saman Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja a kwanan nan, ya yaba da tsarin yin amfani da na’urorin robotics da aka kaddamar.

Masana a fannin sufurin jiragen sama sun bayyana cewa wannan sabon tsarin yin amfani da na’u’rorin tare da gwajin ayyuka da aka gudanar na nufin cewa akwai yiyuwar nan ba da dadewa ba za a dawo da harkokin tashi da saukar jiragen sama.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Kasuwa Sun Koka Kan Shirin Karin Kudin Shiga Jirgin Sama a Najeriya