Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Sake Kwashe ‘Yan Najeriya Dake Amurka Zuwa Gida A Watan Yuli


shugaba buhari

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da shirin maida ‘yan Najeriya dake zaune a Amurka gida, wadanda suka nuna sha’awar komawa.

Sanarwar da gwamnati ta fitar na nuni da cewa, ranar goma sha bakwai ga watan Yuni, za a dauki rukuni na uku na masu sha’awar komawa Najeriya daga tashar jirgin sama ta kasa da kasa dake birnin New York zuwa Abuja.

Sanarwar da ofishin jakadancin Najeriya dake birnin New York ya fitar ta kara da cewa, masu sha’awar zasu sayi tikitin tafiya ta jirgin sufurin kasar Ethiopia kan dalar Amurka dubu daya da dari biyu da hamsin ga masu sha’awar tafiya ta kujerar yaku bayi, ko kuma dala dubu biyu da dari takwas domin zaunawa a kujerar masu hali. Bisa ga sanarwar, wannan kudin na zuwa ne kawai banda dawowa.

Ma'aikata suna sauke kayan aikin jinya daga wani jirgi a tashar Namdi Azikwe Abuja,
Ma'aikata suna sauke kayan aikin jinya daga wani jirgi a tashar Namdi Azikwe Abuja,

Matafiyan suna kuma bukatar nuna takardar shaidar cewa basu dauke da cutar Korona bayan gwaji da bai shige kwanaki goma sha hudu da yi ba. Za a kuma gwada zafin jikinsu sa’oi hudu kafin su tashi. Bisa ga sanarwar, ba za a bari wanda bai cika sharuddan da aka gindaya ya shiga jirgin ba.

Sharuddan da aka gindaya sun kuma bukaci matafiyan su rike sinadarin tsabtace hannu su kuma sa takunkumin rufe fuska a cikin jirgi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG