Yan San Dan Sapain Sun Kashe Mutumin Da Ya Kai Hari A Ranar Alhamis

Yan Sandan Kasar Spain

Karshenta dai 'yan sandan Spain sun harbe mutumin da ake zaton shine direban motar nan da akayi anfani da ita wajen kai harin ranar Alhamis da ya hallaka mutane a Barcelona har lahira.

A karshen tsananin farautar, yan sanda sun kashe Younes Abouyaaqoub a wata arangama dashi a yau Litini a wani kauye da ya shahara wurin noman mai tazarar kilomita 45 daga yammacin Barcelona. Hukumomi sun ce sun harbe shi ne yayin da yake kokarin tada wani abu da ake ganin bam ne a jikinsa.

Wani mawallafi a kan wannan harin ta’addanci na Barcelona yace sun tabbatar da harbe Younes Abouyaaqoub har lahira a Subirats, Yan sanda sun dora a kan shafinsu na Twitter a yau Litinin cewa bayan rahoton farko mutumin da yake a kauyen Subirats yana saye da bam a jikinsa na kai harin kunar bakin wake.

Ministan harkokin cikin gida a Catalan, Joaquim Form, ya fadawa gidan radiyon Catalunya cewar ga dukkan alamu Younes Abouyaaqoub ne ya kai hari da babban motar nan na ranar Alhamis wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 15.