'Yan Siyasar Nijer Sun Bayyana Shakku Game Da Tafiyar Ayyukan Hukumar CENI

A jamhuriyar Nijer ‘yan siyasa sun nuna damuwa game da abinda suka kira jan kafar da ake fuskanta a ayyukan tsare-tsaren zabubukan shekarar 2020 da 2021, lamarin da tuni ya fara haddasa fargaba dangane da yiyuwar wadannan zabubuka akan lokaci.

A taron majalisar sasanta rikicin siyasa wato CNDP da ya gudana a yammacin jiya a karkashin jagorancin Firai Ministan Nijer, Birgi Rafini ne aka bayyana damuwa a dangane da halin da ake ciki a yau sakamakon lura da tsaikon dake tattare da ayyukan rajistar sunayen masu kada kuri’a da ya kamata a fara a ranar 1 ga watan Oktoba.
Hukumar zabe ta kasa da ake kira CENI, a yayin wannan zama ta fayyace ainahin dalilan da suka janyo wannan jinkiri.
Tuni dai wannan al’amari ya fara haifar da shakku a zukatan ‘yan siyasa.
Sai dai hukumar ta CENI ta bada tabbacin daidaita al’amura kafin ranar 15 ga watan da muke ciki.
‘Yan adawa wadanda ba su halarci wannan taro ba na cewa sun san za a rina.
Tsarin jaddawalin hukumar CENI yace a karshen watan Disambar shekarar 2020 ne ake saran gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa hade da na ‘yan majalisar dokokin kasa yayinda za a je zagaye na 2 a watan Fabarairun shekarar 2021.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

A Nijer 'Yan siyasa sun bayyana shakku game da tafiyar aiyukan hukumar zabe