'Yancin Yin Addini Na Fuskantar Kalubale a Duniya - Amurka

Wani rahoton shekara-shekara da gwamnatin Amurka ke fitarwa ya gano cewa ‘yancin addinai na fuskantar kalubale a fadin duniya, musamman a kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kira “inda ake da matukar damuwa,” wato China, Iran, da Koriya ta arewa.

“A China, tilasta canza ra’ayin duk addinai da gwamnatin kasar ke yi na ci gaba da tsananta.

Jam’iyyar Kwaminisancin China ta CCP yanzu tana umurtar kungiyoyin addinai da su yi biyayya da shugananin CCP su kuma cusa akidar kwamunisanci a koyarwa da tsarin addinansu, a cewar sakataren harkokin wajen Mike Pompeo.

Pompeo ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka yi jiya Laraba akan rahoton ‘yancin addinai na kasa da kasa da ma’aiktarar ta fidda na shekarar 2019.

Wannan rahoton na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a wata doka a ranar 2 ga watan Yuni don ciyar da ‘yancin addinai na kasa da kasa gaba.

Trump ya ba ma’aikatar harkokin kasar da Hukumar raya kasashe umurnin kirkiro da shirin da zai maida hankali akan ‘yancin addinai, su kuma ware akalla dala miliyan 50 a kowacce shekara don shirye-shiryen da za su karfafa ‘yancin addinai na kasa da kasa.