Yarjejeniyar Da Aka Kulla Da Jami'ar Bayero Don Bunkasa Harkar Noma

Wata gona da aka girbe masara

Kamfanin Dantata bangaren kula da sarrafa kayayyakin abinci ya kulla yarjejeniya aiki tare da cibiyar Nazari da bincike akan harkokin noma a yankuna masu karancin albarkatun ruwa ta Jami’ar Bayero.

Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya sanya hannu akan daftarin yarjejeniyar yayin da shugaban Kamfanin na Dantata Foods Alhaji Tajudeen Aminu Dantata ya sanya hannu a madadin kamfanin.

Farfesa Jibrin Muhammad Jibrin da ke zaman Darktan Cibiyar nazari da bincike kan ayyukan noma a yankuna masu karanci ruwa wanda ya yi karin haske game da aikace-aikacen cibiyar, ya ce baya ga kamfanin Dantata, suna aiki tare da wasu cibiyoyi da kamfanoni a ciki da wajen Najeriya.

Dama dai masu kula da lamura a bangaren aikin noma, na nanata bukatar samar da yanayin hadaka na aiki tare tsakanin kamfanoni masu sarrafa kayayyakin abinci da kuma cibiyoyin bincike da nazarin dabarun noma a matsayin matakin bunkasa kasa da abinci.

Saurara karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yarjejeniyar Da Aka Kulla Da Jami'ar Bayero Don Bunkasa Harkar Noma