Yau ake sa ran fara aiwatar da wani bangaren dokar hana wadansu kasashe shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump -Washington, DC, 28, 2017.

Jami’an shige da ficen nan Amurka na jiran tsarin yadda zasu aiwatar da umurnin shugaba Donald Trump akan dokar hana mutanen wadansu kasashe zuwa Amirka, dokar da kila a kaddamar da fara amfani da ita da safiyar yau alhamis.

Jami’an ma’aikatar harkokin waje, dana Shari’a da kuma na tsaron Cikin gida kawo yanzu basu da cikakken dangane da wanda ya cancanci shigowa Amurka daga wadannan kasashan 6 da dokar ta shafa, wanene kuma bai cancanta ba.

Kasashen dai sun hada da Iran, Libya, Somalia, Sudan, Syria da kuma Yemen.

Ranar Litinin da ta gabata, babbar Kotun Amurka ta sake maido da wani bangaren dokar da wadansu kananan kotuna suka dakatar da farko, suna dogara ga abinda dokar kasa tace dangane da batun tsaro.

Kotun ta bada umurnin cewa sai an yi zama akan wannan batu, amma kafin nan bakin da za a bari su shigo sai sun nuna cewa suna da wadansu ‘yan uwa na kud-da-kud kafin a barsu su shigo kasar.

Sai dai kotun bata fayyace ma’anar wannan dangantakar ta kud-da kud ba.