Yau Amurka Ke Bukin Samun 'Yan-cin Kai Daga Mulkin Ingila

Shugaba Trump ya sanar da cewa, za a gudanar da sarawar, da ake yi wa Amurka, don nuna muhimmancin karfin ikon sojojin kasar, kuma za a nuna jawabinsa daga kan matakalar benen Lincoln Memorial.

A yau Alhamis, Amurka ke bukin zagayowar ranar samun ‘yancin ta, a lokacin da ake wasan harba wuta, a sama da dare da ake kira Fireworks a turance, iyalai da abokan arziki kuma, su tattaru don bikin ranar a fadin kasar, bayan haka, shugaba Donald Trump, zai yi wani dan jawabi ga al’ummar kasar.

Bukukuwan ranar 4 ga watan Yuli, na tunawa, da lokacin da Amurka, ta ayyana samun 'yancin kai daga Ingila, a shekarar (1776). A babban birnin kasar, wato Birnin Washington, bukin ranar ya janyo dubban mutane, zuwa wurin da ake kira National Mall a birnin.

Jiya Laraba, Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa “za a yi bukin da ba a taba yin irin sa ba.”