Yau Take Ranar Da CDC Da MDD Suka Ware Domin Tsaftar Hannaye

Global Hand Washing Day

Yau 15 ga watan Oktoba rana ce da kungiyoyin tabbatar da tsaftar hannaye a Duniya tare da amincewar Majalisar Dinkin Duniya suka kebe, domin yin yekuwa wajen ganin kasashen Duniya sun bi umurnin a rika wanke hannu akai akai, domin kawar da cututtuka masu saurin yaduwa, irin su Kolara da Taifod da zazzabi Lassa da Mura Mai tsanani da kuma Sankara.

A Najeriya, cibiyar kula da cututtuka ta dauki matakin amfani da kafafen yada labarai na gargajiya da kuma na yanar gizo wajen fadakar da al'umma.

Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta tattauna da mataimakiyar Darekta a fannin shirye shirye da wayar da kan al'umma ta cibiyar, Dakta Fatima Saleh don jin tabakinta game ta mahimmancin wannan rana game da cututtuka.

A saurari cikakken rahoto daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dinkin Duniya: Yau Ne Ranar Tsaftar Hannaye