Yawan Hare-Hare Na Haifar Da Zaman Dardar a Mali

A yayin da kasar Mali ke fara zaman makoki na kwanaki uku a jiya Litinin, bayan da aka kashe mutane 54 a wani harin da aka kai a makon da ya gabata, mazauna yankin sun nuna fargaba game da karuwar tashe-tashen hankali, yayin da wasu manazarta suka yi kira da a kara kaimi wajen ayyukan tattara bayanan sirri da hadin kai.

Yayin da yake magana kan wannan hari, wanda aka kai a ranar Juma’ar da ta gabata, wani mai fafutuka da ake kira Dr. Abdoul Kane Diallo, ya ce "ba za mu zura ido muna kallo a kowacce rana mutane na kawo hari akan sansanoninmu ba, suna kashe daruruwan sojojinmu."

Diallo ya nuna fushinsa a fili, saboda a cewars shi, duk da cewa an sanar da hukumomi nan da nan a lokacin da aka kai harin da rana, "amma abin mamakin shi ne, babu wani dauki da aka kai."

Tuni dai kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS ta dauki alhakin kai harin.