Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Ta Yi Wa Magoya Bayanta Albishir


Wani sashin yada labaran kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS, ya yi wa magoya bayan kungiyar albishir cewa, akwai wani babban labari mai dadi da zai fito,

Wannan ita ce sanarwa ta farko da kungiyar ta fitar, tun bayan mutuwar shugabanta Abubakar Al Baghdadi a wani samame da Amurka ta kai a ranar Lahadi.

Tun da tsakar ranar jiya Laraba, sashin yada labaran da ake kira Al Furqan Foundation, ya fara watsa labaran, amma ba tare da ya fadada bayanansa ba.

Wata kungiya mai suna SITE da ke tattara bayanan sirri, ta ke kuma bin diddigin kafofin sadarwar kungiyar masu ikrarin jihadin, ta ce tuni magoya bayan ISIS suka fara yada labaran a kafafen sada zumunta.

Yayin da wasunsu ke fatan jin cewa Al Baghdadi na raye, wasu na jiran su yi bikin jihadin da suke ikrarin ya yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG