Za A Dauki Matakan Dakile Bakin Haure Dake Bi Ta Nijar

A woman, who lost her father in World War II, holds a dove before releasing it as she prays for the war dead at the Yasukuni Shrine in Tokyo on the 69th anniversary of Japan's surrender in World War II.

Kasar Spain da kungiyar CDEAO (ECOWAS), zasu bayar da fiye da kashi 90 cikin n100 na kudaden gudanar da wannan gagarumin aikin hana bakin haure shigewa
Jamhuriyar Nijar, wadda ke da bakin iyaka mai dan karen tsayi da girma, da kuma makwabtaka da wasu daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya, ta fi kowace kasa a nahiyar gahnin bakin haure masu bi ta cikin kasarta a yunkurinsu na satar shiga cikin kasashen Turai.

Ganin irin wannan matsala da kasar take fuskanta, da kuma ganin cewa ita kanta tana samar da bakin hauren dake kokarin satar shiga kasashen na Turai, ya sa hukumomin kasar tare da hadin kan Kungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, da kuma kasar Spain, zasu kaddamar da wani sabon shirin dakile kwararar irin wadannan bakin haure.

Shirin da zai ci kudi mai dan karen yawa, zai shafi horas da jami'an tsaro da dogarawan bakin iyaka, tare da samar musu da kayan aiki na zamani ta yadda zasu iya tarewa da juya akalar irin wadannan bakin hauren.

Za a shafe tsawon watanni 18, ko shekara daya da rabi, ana aza harsashin wannan sabon shirin wanda ba kawai zai ma dakile irin bakin hauren dake bi ta cikin kasar ba ne, zai kara karfafa tsaron bakin iyaka da kuma kasar ta Nijar baki daya.

Wakilin sashen Hausa, Abdoulaye Mamane Ahmadou, ya aiko mana da karin bayani daga Yamai.

Your browser doesn’t support HTML5

Matakan Shawo Kan Matsalar Bakin Haure Dake Bi Ta Jamhuriyar Nijar Zuwa Turai - 2:37