Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijer Ta Kwace Kwangila Daga Kamfanin Rasha


Shugaban Junhuriyar Nijer, Muhammadou Issoufou
Shugaban Junhuriyar Nijer, Muhammadou Issoufou

Kimanin shekaru biyu ke nan da gwamnatin Niher ta baiwa wani kamfanin kasar Rasha kwangilar gina madatsun ruwa.

A wani taro da manema labarai da Frayim Ministan Nijer ya kira ya shaida masu cewa gwamnati ta karbe kwangilar gina madatsun ruwa da ta baiwa wani kamfanin kasar Rasha kimanin shekaru biyu da suka wuce sabili da wasu dalilai da suka fi karfinsu.

A cikin jawabinsa Frayim Ministan ya ce a cikin shekaru biyu da kamfanin ya soma kwangilar aikinsa bai kai kashi bakwai ba cikin dari duk da yawan jawo hankalin kamfanin da suka sha yi.Ya ce kawo yanzu ya kamata a ce aikin ya haura fiye da kashi arba'in cikin dari. To amma ba haka lamariin yake ba. Ya ce idan aka lura akwai gazawa da kayan aiki da dai makamantansu wanda hakan zai yi wuya a cimma dogon burin kasar ta Nijer idan aka bar kwangilar hannun kamfanin. Kwangilar ta kai kimanin sefa sama da miliyan dari hudu a yayin da aka ce ita gwamnatin Nijer bata baiwa kamfanin kudi fiye da kashi takwas cikin dari ba.

Kungiyoyin fararen hula a kasar sun yi murna da jin labarin. Sai dai sun ce ya kamata mahukuntar Nijer su yi hattara a kan yarjejeniyar, su san dabarar da zasu bi domin kamfanin ko kasar Rasha na iya kai kara a nahiyar turai.

Ga karin bayani na Abdullahi Mamman Ahmadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG