Za a Kaddamar Da Shirin Tantance Bayanan Bogi Game Da Cutar COVID-19

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shiri na yaki da bayanan bogi da ake yadawa a shafukan sada zumunta wadanda suka shafi annobar coronavirus.

Sakataren Majalisar Antonio Guteress ya fada a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis cewa, “babu yadda za mu nade hannayenmu muna kallo wasu suna yada karerayi tare da jefa fargaba a zukatan mutane da kuma kiyayya.

A kwanakin baya, Guterres ya nuna damuwa kan yadda matsalar nuna wariya, da kalaman batanci da kuma nuna kyama dangane da cutar coronavirus, suke yaduwa a yanar gizo.

Tun dai bayan bullar cutar COVID-19, ake ta samun yaduwar labaran da ke danganta cutar da wata makarkashiya a shafukan yanar gizo da sakonnin da ake aikawa ta hanyoyin tes na shafukan sada zumunta.

Wannan shirin da majalisar ke shirin kaddamarwa, na kokarin ya kai ga miliyoyin mutane a duk fadin duniya inda za a yada shi cikin harsuna da dama akan cutar COVID-19.

Shirin wanda aka mai taken “verified” wato abinda aka tabbatar, zai dogara ne ga dumbin bayanan da za a rika watsawa a kullum a sassan duniya, wanda zai zo a kimtse domin yadawa a shafukan sada zumunta dauke da rahotannin da Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar lafiya ta WHO suka tabbatar da sahihancinsu.