ZABEN2015: Zabe Ya Zama Dole - inji 'Yan Majalisa

  • Ibrahim Garba
Yayin da ake ci gaba da cece kuce kan zaben Najeriya, Majalisar Tarayyar Najeriya tace ba za a sake dage zaben ba.

Majalisar Tarayyar Nijeriya ta ce za ta sa ido sosai ta ga cewa ba a samu wata matsala ba a zaben Nijeriya da ke tafe.

Mataimakin Shugaban Kwamitin Zabe na Majalisar Tattawa Sanata Alkali Abdulkadir Jajere ya gaya ma wakiliyarmu a Abuja Madina Dauda cewa Majalisar ta ji kishin-kishin din cewa wasu na so su gabatar da wani kuduri na dage zaben ma kwata-kwata, wanda hakan in ji Sanata Jajere, wani “mushen kare” ne ake so a shigar Majalisar kuma sun sha alwashin ba za su ji warinsa ba balle ma har su ganshi.

Ya ce masu kulle-kullen a dage zaben sun dogara ne ga shafi na 135, wanda ya ce idan ana yaki a wani bangare na kasa, to Shugaban Kasa na iya neman izinin Majalisar na dage Zabe zuwa wata shida; a kara zuwa wani wata shidan a kuma kara zuwa wani wata shidan muddun da bukatar hakan. To amma Sanata Jajere ya ce ba za su lamunta da hakan ba a Majalisa.

Sanata Jajere ya ce su ma sun a da tanaje-tanajen kundin tsarin mulkin da za su dogara da su wajen yin watsi da wannan kullalliyar saboda a samu yin zaben.

Shi kuwa Hon Jagaba Adam Jagaba na Majalisar Wakilai, ya ce ga dukkan alamu, abin sai an hada da addu’a. Amma y ace bai kamata a yi tunanin cewa ba za a yi zaben ba. Sakataren Jam’iyyar APA Sama’ila Umar Sifawa kuwa kira yak e ga gwamnati ta dau matakan da su ka dace saboda sassautar ma ‘yan Nijeriya wahalhalun da su ka riga su ka shashsha.

Your browser doesn’t support HTML5

Zabe Ya Zama Dole - inji 'Yan Majalisa