Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Boko Haram ta Lashi Takobin Hana Zabe


A wani sabon bidiyo da ya fitar shugaban kungiyar Boko Haram yace kungiyarsa zata hana yin zabe.

Kungiyar Boko Haram ta Najeriya, tayi barazanar tarwatsa zabukan da ake shirin gudanarwa a kasar, da aka dage zuwa watan gobe sabili da tada kayar baya da kungiyar ke yi.

A cikin wani sabon bidiyo da ta fitar a yanar gizo ranar Talata da maraice, shugaban kungiyar Abubakar Shekau yace koda tashin hankalin zai hallaka mayakansa, Allah ba zai bari a gudanar da zaben ba.

Kungiyar mayakan ta sha gargadin jama’a kada su fita zaben shugaban kasa da na‘yan majalisar da za a gudanar, wanda yanzu aka tura zuwa ranar 28 ga watan Maris. Tun farko an yi shirin gudanar da zaben ne ranar goma sha hudu ga wannan watan na Fabrairu daga baya aka tura gaba.

A halin da ake ciki kuma, rahotanni daga kudu maso gabashin Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa, akalla mutane 20 aka kashe bayanda wani jirgi da ba a tantance ba ya sako bom kan wani kauye dake kusa da kan iyaka da Najeriya. Najeriya ta musanta kai harin da ya faru a yankin da kungiyar Boko Haram ke kai hare hare.

Rundunar sojin Najeriya tace ta kashe sama da mayaka dari uku ta kuma sake kwace garuruwa goma sha daya daga hannun kungiyar Boko Haram a hare haren da ta kaddamar ta kasa tun daga ranar Litinin.

Babu wata majiya da ta tabbatar da wannan ikirarin.

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG