ZABEN 2015: Kiristoci da Musulmai Sun Yi Azumi da Addu'o'i a Jihar Adamawa

Jihar Adamawa

Jiya Alhamis al'ummar Adamawa kiristoci da musulmai suka kammala yin azumi da addu'o'in rokon Ubangiji ya tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe

Alhaji Gambo Jika na kungiyar Jama'atul Nasril Islam yace sun shirya tarukan addu'o'in ne domin samun zaman lafiya tsakanin al'ummomin Najeriya musamman ganin yadda harkokin zabe ke son raba kawunan 'yan kasar.

Yace makasudin taron shi ne su kawo karshen addu'o'in da suka dukufa suna yi yau fiye da wata uku. Allah yasa a yi zabe lami lafiya a kuma kareshi lami lafiya. Allah kuma ya bayar da shugabanni nagari masu tausayin talakawa.

Ya kira mutane su zabi mutumin da zai kawo cigaban al'umma da kasa. Kada su bi rudu na wasu mutane, musamman yin anfani da wasu banbance banbance na kabilanci ko addini.

Shi ma a nashi tsokacin wani mai bishara a Yola Thompson Garba yace dole ne a kai zuciya nesa a kuma cika da yin addu'a musamman a wannan lokaci na zabe da kasar bata taba fuskantar irinsa ba. Yace kodayaushe fastoci suka taru a mijami'u addu'o'i suke yi. Sabili da haka ya kira jama'a su guji abun da zai kawo rikici lokacin zabe. Kada a yi abun da zai kaiga shiga yaki.

Su ma 'yan jarida suna kiran 'yanuwansu su guji yada labarun da zasu kawo rudani ko tayar da hankulan jama'a.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN2015: Kiristoci da Musulmai Sun Yi Azumi da Addu'o'i a Jihar Adamawa - 3' 46"