Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Jonathan da Buhari Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, Maris 26, 2015.

A karo na biyu cikin 'yan kwanaki kadan Shugaba Jonathan na PDP da Janar Buhari na APC sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya lokacin zabuka da ma bayan an kammala.

Jiya aka yi wata ganawa tsakanin Shugaba Jonathan da Janar Buhari a karkashin shugabancin kwamitin wanzar da zaman lafiya da Janar Abdulsalami Abubakar ke jagoranta domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da ma bayansa..

'Yan takaran biyu sun rattaba hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya cewa zasu tabbatar an samu zaman lafiya yayin da ake yin zabukan da kuma bayansu. Wannan yarjejeniyar ita ce ta biyu cikin 'yan kwanakin nan.

Idan ba'a manta ba tun can farko kasashen waje suka taru suna nazarin yadda za'a tabbatar da zaman lafiya a kasar yayinda ake yin zabukan da bayan an kammalasu.

Wannan yarjejeniyar ta biyu ta kara jaddada mahimmancin amincewar 'yan takarar da sakamakon zabukan su kuma sa kasar Najeriya kan gaba a zukatansu fiye da kowane ra'ayinsu ko na jam'iyyunsu.

'Yan takaran sun rattaba hannu akan yarjejeniyar inda suka kara bada tabbacin cewa babu gudu ba ja da baya zasu dauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da cewa an yi zabukan cikin lumana da kwanciyar hankali. Zasu amince da sakamakon koma wanene yayi nasara ko bai yi nasara ba.

Wannan yarjejeniyar ta biyo bayan matsin lamba daga tarayyar Turai da wasu kasashen Afirka da suka ziyarci Najeriya akan batun zaben. Sun gana da duk 'yan takarar a kokarin tabbatar da zaman lafiya lokacin zaben da ma bayansa. Suna fatan irin tashin hankalin da aka samu a shekarar 2011 bai sake faruwa ba.

Saidai 'yan takarar kananan jam'iyyu sun yi korafi akan rashin gayyatarsu su rattaba hannu akan irin wannan yarjejeniyar ta zaman lafiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG