ZABEN 2023: Yadda Jinkirin Sa Hannu A Kwaskwarimar Dokar Zabe Ka Iya Kawo Cikas

Taron Takarar Zabe A Najeriya

'Ƴan siyasa da Masana Harkokin shari’a na ci gaba da yin sharhi dangane da jinkirin sanya hannu akan kwaskwarimar dokar zaben Nigeria da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ke yi.

Bayanai dai sun nuna cewa, shugaba Buhari ya tura kudirin dokar ga ofishin babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a na Najeriya domin bashi shawara a kan wannan doka da Majalisar kasar ke bukatar ganin ya rattabawa hannu,

Jigon APC a Nigeria kuma dan Majalisar wakilan Najeriya Shele Sale Rijau yace yana mamakin yadda shugaba Buharin ke jinkirin sanya hannu a wannan kudirin doka.

Kudurin dokar dai yana bada dama ga jam’iyyun siyasa su kara yawan masu kada kuri’a a zaben fidda ‘yan takara na jam’iyyu da ake kira daliget da a ranar lahadin jam’iyyar PDP ta fara gudanar da zaben fidda ‘yan takarar ta da zasu shiga zaben neman Mukaman Majalisun jihohi.

Ku Duba Wannan Ma Shekarau Ya Fice A APC, Ya Shiga NNPP

A yanzu dai masana kundin tsarin mulkin kasa na ganin matakin na shugaba Buhari tamkar tauye hakkin Damokradiyya ne kuma yana iya haifar da shari’u bayan kammala zabubbuka.

A yanzu dai ‘yan Najeriya sun zura idanu a fadar shugaban kasa domin ganin ko wannan doka zata samu shiga ko za a zuba ta a kwandon shara.

Saurari cikaken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN 2023:Yadda Jinkirin Sa Hannu A Kwaskwarimar Dokar Zabe Ka Iya Kawo Cikas-3:00"

Ku Duba Wannan Ma Zaben 2023: Ya Cancanta Goodluck Jonathan Ya Tsaya Takarar Shugaban Kasa?