Zamu Magance Matsalar 'Yan Ta'adda A Kasashen Afrika

Kwamandan Rundunar Sojin Kasar Liberia Ya Nuna Damuwa Akan 'Yan Ta'adda Da Suke Shigowa Kasar Da Yadda Za'a Magance Su.

Mukaddashin shugaban rundunar sojin kasar Liberia, ya nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda suke shiga cikin kasar daga kasashe makwabta.

Yayi wadannan kalaman ne yayin wata ganawa ta musamman da Muryar Amurka, Kwamandan Sajent Manjo Karmoh Duke Freeman, ya ce ya zama dole a dauki matakin kara dakarun kasar, domin hakan ya zama sako ga ‘yan ta’adda da ke aikace-aikacensu a kan iyakokin kasar.

Ita dai rundunar dakarun kasar ta Liberia, mai yawan sojoji dubu biyu, an sake hada ta ne bayan yakin basasan da ya kawo karshe a shekarar 2003.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke taimakawa kasar a baya, sun janye a farkon shekarar nan, lamarin da ya bar kasar cikin yanayi na rashin cikakken tsaro.