Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kidaya Ta Nijar Za Ta Dau Alkaluma a Gidaje Dubu 3


Taswirar Nijar
Taswirar Nijar

A wani yinkuri na neman sanin samfur din yanayin gidaje a Janhuriyar Nijar, hukumar kidaya za ta dau alkaluma a dubban gidaje a wurare wajen 250 a kasar.

Ma'aikatar kididdiga ta Nijer reshen jahar Dosso, ta gudanar da taron fadakarwa, da ya hada hukumomi na birane da sarakunan gargajiya da limamai da manyan malamai, on samo wata kididiga ta iyalai daban - daban gameda halin rayuwarsu domin tantance wadanda ke cikin matsanancin talauci domin su kansu, su dauki matakan kyautata rayukansu da irin yanda hukumomin kasar ke iya agaza musu.


Magatakardan offishin gwamnan jahar Dosso Malam Assumane Amadu shine ya jagoranci bukin soma wannan taron a Birnin Dosso, kuma a lokacin da yake jawabin soma taron yana mai cewa za a yi wannan aikin ne saboda amfanar jama'a. Don haka ya bukaci hadan kan jama'ar.


Labarun da ke gare mu a halin yanzu, sun nuna cewa tsawon wadannan watanin 3, tawagogi 15 na ma'aikatar kididdiga ta wannan kasar kowace da durobanta da shugaban tawagar da masu kididiga 3 za su ziyarci dukkan fadin Nijer domin tantamnawa da iyalai dubu 3 a wurare 250 a dukkan fadin Nijer.


Ga wakilinmu a Birnin Konni Harouna Bako da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG