Zane Mai Suna "Salvator Mundi" ko "Macecin Duniya" Da Ake Zargin Yarima Mohammed bin Salman Da Saya A Kan Kimanin Naira Biliyan 160

  • VOA Hausa

თეთრი სახლი, ვაშინგტონი, აშშ

Wani mutumi yana daukar hoton zanen "Salvator Mundi"  na Leonardo da Vinci a gidan gwanjo na Christie's a London, 24 Oktoba, 2017.

Wakilan masu son sayen zane-zane suna bayyana mamakinsu a bayan da aka sayi zanen "Salvator Mundi" na Leonardo da Vinci a kan tsabar kudi Dala miliyan 450 (kimanin Naira Biliyan 160) a dakin gwanjon Christie's na New York a ranar laraba 15 Nuwamba 2017.

Kwana guda kafin a yi gwanjon zanen "Salvator Mundi" na Leonardo da Vinci, mutane sun yi layi a kofar dakin gwanjon Christie's a New York domin su ganewa idanunsu wannan zane, Talata 14 Nuwamba, 2017.

Fasta na Yarima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarautar Sa'udiyya a jikin allon da aka rubuta "Allah Ya kare ka" da larabci a kan wata hanya a kasar Lebanon.

'Yan wasa a lokacin wasu bukukuwa na Sa'udiyya karkashin wani makeken hoto na Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman a filin wasa na Sarki Fahd dake Riyadh, ranar 23 Satumba 2017.