Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Najeriya Sun Koka Akan Matsalar Man Fetur


Fuel Scarcity in Nigeria

Yayin da ake haramar bukukuwan kirsimeti da kuma na sabon shekara, wata matsalar da ka iya shafan bukukuwan a bana a Najeriya, ita ce ta karancin mai, lamarin da ya sa masu ababen hawa ke kwashe sa’o’I akan layin sayen mai.

Wasu masu ababen hawa sun koka akan yadda suke shan wahala kowacce shekara musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti saboda matsalar mai, amma da lokacin ya wuce sa man ya wadatu.

A yayinda na gwamnati ke saidawa, akwai wasu gidajen man dake wuce makadi da rawa. Alhaji Usaini Abbkar, direban mota ne wanda ya bayyana cewa gidajen mai dayawa suna da man amma basa so su saida. Ya kuma ce su kan boye sai da dare su saidawa ‘yan bumburutu.

Lokuta dayawa akan zargi dillalan man fetur masu zaman kansu na IPMAN da masu dakon mai akan cewa su ke boye man a wannan lokacin domin cin kazamar riba. Amma shugabannin kungiyoyin biyu sun sha musanta wannan zargin.

Alhaji Abdulmalik Bello, mataimakin shugaban NATO a shiyar Yola wanda kuma kusa ne a kungiyar IPMAN, yace rashin sani ne ke sa ake yi masu wannan zargin. Babban dalilin matsalar man a yanzu shine babu isasshen man a kasa saboda matatan man Najeriya ba asa iya sarrafa man da zai ishi ‘yan Najeriya.

Ga karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul'aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

Labarai masu alaka

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG