Zanga Zanga Ta Barke A Turkiyya Dalilin Tsige Wasu Jami'an Gwamnati

Yan Sanda na kama wani mai zanga zanga a Turkiyya

Rigima ta kaure a kasar Turkiyya tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga a Kudu maso Gabashin Turkiyya, bayan da gwamnati ta fitar da sanarwar cewa ta maye gurbin wasu zabebbun kantomomi da shugabannin kananan hukumomi har 28, a wasu garuruwan Kurdawa.

Maye gurbin zabebbun jama’an dai ya biyo bayan zargin alakarsu da wasu kungiyoyin ta’addanci da gwamnati ke yi, a cewar ministan harkokin cikin gida na Turkiyya.

Ashirin da hudu daga cikin wadanda aka cire ana zarginsu ne da alaka da kungiyar adawa ta Kurdawa da ake kira PKK, yayinda kuma sauran Hudun kuma ake zarginsu da cewa suna da alaka da kungiyar magoiya bayan Gulen, mutumen da ake zargi da shirya yunkurin juyin mulkin da bai sami nasara ba na watan Yuli wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da mutane 270.