Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Ta Soke Kamfen Dinta Na Yau A Jihar California


Hillary Clinton
Hillary Clinton

'Yar takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar democrats ta Amurka, Hilary Clinto, ba zata yi kyamfen yau Litinin ko gobe Talata ba a jihar California bayanda likitoci suka tabattarda cewa tana fama da ciyon harakari.

Kwamitin kyamfen din Hilary din ya bada sanarwar cewa Likitarta ta bincike ta bayanda aka ga tana fama da tari.

Likitar mai suna Lisa Bardack ta bayar da wannan sanarwar ne a jiya Lahadi, bayan da Hillary ta bar wajen bukin tunawa da harin 11 ga watan Satumba a birnin New York inda ta nemi faduwa sai da aka taimaka mata wajen iya shiga motarta.

Mukarabbanta sun tuka ta zuwa gidan ‘yar ta Chealsea domin ta samu ta huta, daga baya kuma an ga Hillary ta fito waje, inda aka ga alamun ta samu hutu sosai. Ta rungumi wata yarinya karama akan titi tana kuma ‘dagawa magoya baya hannu.

A lokacin da take shirin tafiya cikin mota, Hillary tace “ na murmure sosai yanzu, wannan rana ce mai armashi anan birnin New York.”

Likita Bardack, tace Hillary mai shekaru 68 da haihuwa, ta fuskanci wannan matsalar ne a sakamakon zafin rana da kuma rashin isasshen ruwa a jikinta.

Har yanzu dai jam’an kamfen dinta basu sanar da cewa ba ko za a soke wasu abubuwan da aka shirya mata na hidmar kyamfen din ta ba.

Tuni dai abokin adawar ta Donald Trump yace Hillary ba ta da karfin jiki da zata iya rike shugabancin Amurka. Wasu masu goyon bayan sa kuma suna kokarin mayar da rashin lafiyarta a matsayin wata matsala a kamfen.

Trump mai shekaru 70 da haihuwa ya fitar da wata wasika daga likitansa a shekarar da ta gabata yana mai cewa shine “Mutum mafi lafiya da za a taba zaba ya zama shugaban kasa” a tarihin Amurka.

XS
SM
MD
LG