Zanga Zangar Belarus Ta Sake Kunno Kai A Ranar Haifuwar Shugaba

Protest in New York against Belarus leader Aleksandr Lukashenko

Dubun dubatar masu zanga zanga 'yan kasar Belarus sun fito jiya Lahadi ranar zagayowar haihuwar Shugaban kasar suna bukatar ya sauka daga mulki.

Dauke da tutoci masu launin ja da fari, alamar nuna adawa, masu zanga zangar sun yi cincirindo a zagayen gidan shugaba Lukashenko suna kuma fuskantar jami’an tsaro dauke da makamai, suna kuma tsaye a gaban motocin gidan yari da mesar ruwa.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce an kame akalla masu zanga zanga 140 a jiya Lahadi kafin su tarwatsa cikin lumana.

Alexander Lukashenko, wanda ya cika shekaru 66 a jiya lahadi, ya yi shekaru 26 yana mulki, a ranar 9 ga watan Agusta aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe da ake zargi na cike da magudi, zargin da ya musanta.

Babbar 'yar takara a jam’iyar adawa Sviatlana Tsikhanouskaya, ta ce sam bata amince da sakamakon zaben ba. Ta bar kasar zuwa Lithuania saboda abinda ta bayyana da kare lafiyar ‘ya ‘yanta.