A kasar Niger dakarun sojan Amurka sunce zasu ci gaba da taimakawa sojan Niger duk da harin da aka kai da ya halaka sojojin Amurka hudu.
A Hong Kong kuma an saki yan gwagwarmaya masu fafutukar demokratiya Joshua Wong tare da Nathan Law akan baili bayan kamasu da aka yi a shekarar 2014 saboda rawar da suka taka wajen yin zanga zanga.
A Kano, wata yarinya ‘yar shekaru 13 da aka yi wa fyade har ta haihu amma kotu tayi watsi da karar da aka shigar saboda babu cibiyar gwajin kwayar halittan dan adam na DNA da ka iya tantance mahaifan yaro
Firayin Ministan kasar Japan Shinzo Abe ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a karsahen makon da ya gabata da tazara mai yawa, kuma ya sanar da cewa zai yi garambawul a kundin tsarin mulkin kasar.
Wasu ‘yan kunar bakin wake su 3 sun kashe mutane 13 a birnin Maiduguri a wani hari na baya baya da ‘yan boko haram suka kai a arewa maso gabashin Najeriya.
Iraq: Sojin Iraqi sun kwato Yankin Kirkuk mai wadatar mai bayan da suka yi bata kashin sa’o’i uku da Mayakan Kurdawa na Permerga
Togo: Masu zanga-zanga da jami’an tsaro sun yi arangama a Lome gabannin wata zanga-zanga da ‘yan adawa suka shirya inda suke ganin gwamnatin ba ta kan ka’ida.
Kasar Congo ta zamaa daya daga cikin kasashe 15 da aka zaba ta zama memba na mambobin majalisar dinkin duniya masu kare hakin bil adama daga cikin kasashe 47 duk da sukarda suke sha daga kasar Birtaniya, Amurka da dai wasu kungiyoyi.
A kasar Somaliya dubban mutane ne suka yi zanga zanga a babban birnin kasar wato Mogadishu suna Allah waddai akan wadanda suka kai harin bam da ya kashe akalla mutane 300 da kuma jikkata wasu fiye da 400.
A kasar Angola kuma sabon shugaban kasar Joao Lourenco ya yi jawabinsa na farko a gaban majalisar dokokin kasar.
A Afghanistan wani dan kunar bakin wake dake cikin wata mota da wani dan bindiga sun kai hari a babban oficin yan sandan dake wani lardi, suka kashe mutane 12 da jikkata wasu 60.
Kwamandan yaki Da Boko Haram a Arewa Maso Gabashin Najeriya, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana nasarorin da soji ke samu a taro da manema labarai a Maiduguri.
Ana sa ran yin zaben fidda gwani a Laberiya, tsakanin tsohon zakaran kwallon kafa George Weah, da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai, ganin babu wanda ya sami kashi 50 cikin 100 da ake bukata don cin zabe.
Mace-macen da suka faru sanadiyar mummunan harin ta’addancin da aka kai a birnin Mogadishu ya kai 270, mutane fiye da 300 kuma sun jikkata. Gwamnatin kasar tana zargin al-Shabab.
Domin Kari