Dr. Ibrahim Bello, babban jami’i a sashen jini na asibitin kasa da ke Abuja yayi mana karin bayani a game da cutar ta Anemia da hanyoyin kare kai.
WHO ta ce rashin abinci mai gina jiki, cuttuka masu yaduwa daga mutum zuwa wani, cututtuka masu tsanani, jinin al’ada mai zuba da yawa, matsaloli a yayin da mace take da ciki da kuma cututtuka da ake gadonsu suna daga cikin abubuwan da ke kai ga kamuwa da anemia.
Akaron farko tun bayan annobar korona, shugaba Kim Jong Un ya kai ziyarar aiki Rasha inda ake sa ran kasashen biyu za su sabunta dangantakar kawance tsakaninsu.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ana kamuwa da cututtuka sama da 200 ta hanyar cin abincin da ke dauke da kwayoyin cutar bacteriya, biros ko kuma sinadarai masu illa.
Kowace shekara, ’yan kungiyar Zumunta suna haduwa a wuri guda domin sada zumunta da kuma duba yiwuwar yadda zasu taimaka wa juna da kuma yadda zasu bada nasu gudunmawa wajen cigaban Najeriya. Sannan yin hakan yana taimaka wa yaran da suke Haifa wajen fahimtar al’adu da mahimmancin hadin kai.
Rubiales ya shiga matsala bayan da ya sumbaci wata 'yar wasan kasar ta Sifaniya a labbanta ba tare da izininta ba a lokacin da ake bikin ba da kyautukan lashe kofin gasar mata ta duniya da kasar ta yi.
A Nijar, inda aka samu juyin mulki sannan aka kakaba wa kasar jerin takunkumai, ayyukan kungiyoyin jinkai ya ragu sossai, lamarin da ya jefa al’ummomin da suke ba su tallafi cikin takaici.
Masu ruwa da tsaki a harkar kanana da matsakaitan masana'antu sun gana a Kano domin samo mafita akan matsalolin da suke hana 'yan kasuwa samun tallafi a arewacin Najeriya.
Karancin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya na shafar hanyoyin samun kulawar mutane, da ingancin kulawar da suke samu, da kuma yawan mutanen dake mutuwa sakamakon cututtuka a nahiyar.
Kwararru sun ce ana samun karuwar mutane masu kananan shekaru tattare da cutar bugun jini a fadin duniya sannan wasu dalilai da suke haifar da wannan yanayi sun hada da kiba mara kima, hawan jini da kuma cutar sukari wato diabetes.
Kungiyar ASUU ta sha kaya a kotu, a yunkurinta na ganin ta haramta kungiyoyin al’umma biyu CONUA da (NAMDA) wadannda suka kasance kishiyoyinta.
Duk da cewa suna kusa da tushen wutar lantarki na Kainji dake jihar Neja a Najeriya, garuruwan da suke gabar ruwan da ke samar wutar lantarki a kasar suna zaune ne cikin duhu.
Yayin da ake fama da matsanancin zafin ranar bazara, wutar dajin dake ci a yankin Meditrranean ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
Bisa binciken cibiyar kiwon lafiya ta Amurka, samun isashen bacci yana inganta yadda kwakwalwa take aiki, yanayin farin ciki da kuma lafiyar ka. Rashin sammun wadatacen bacci na kara barazanar kamuwa da cututtuka da matsalolin lafiyar jiki.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce matsananciyar damuwa mai alaka da aikin da mutun ke yi, ta na samuwa ne sakamakon irin yanayin aikin da mutun ke yi, ko kuma yanayin da ya ke yin aikin, ko jadawalin aikin na shi ko kuma rashin samun damar karin girma ko cigaba a wurin aiki.
Domin Kari