Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Kim Jong Un Ya Kai Ziyarar Aiki Rasha


North Korea Russia
North Korea Russia

Akaron farko tun bayan annobar korona, shugaba Kim Jong Un ya kai ziyarar aiki Rasha inda ake sa ran kasashen biyu za su sabunta dangantakar kawance tsakaninsu.

Kafar yada labaran KTA KCNA, a yau Laraba ta ruwaito cewa Shugaban KTA Kim Jong Un ya ce ziyarar shi zuwa Rasha alama ce da ke nuna mahimmancin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu

Rahotannin kafar yada labaran KTA KCNA sun ce a jiya Talata ne Kim ya isa Rasha cikin wani jirgin kasa da ba na fasinja ba domin tattaunawa da shugaban kasar Vladimir Putin a daidai lokacin da Amurka take yi wa kashen biyu gargadi kan cinikin makamai tsakaninsu. Kim Jong Un ya ce ziyararsa a Rasha alama ce ta matsayar jam’iyyarsa ta ‘yan gurguzu ta WPK da kuma gwamnatin kasarsa a game da yadda suka bai wa dangantakarsu da Rasha fifiko.

Wasu hotuna da KCNA ta yada sun nuna sa’adda Kim ya ke gaisawa da manyan jami’an gwamnatin Rasha bayan da ya isa tashar jirgin kasa a garin da ke kan iyaka da Rasha da safiyar jiya Talata.

Sannan a wani hoton kuma, Kim yana gaisawa da ministan ma’adinan kasar Alexander Kozlov.

Ba a san takamaiman wuraren da zai je (abubuwan da zai yi ba ) ba amma kamfanin dillancin labaran Japan Kyodo da kafar yada labaran KTK sun bada rahoton yiwuwar ganawar shi da Putin a Vostochny Cosmodrome a gabashin Rasha.

Wannan ita ce ziyarar Kim ta farko zuwa Rasha cikin shekaru 4 kana ziyararsa ta farko zuwa wata kasar ketare tun bayan matsalar lafiyar da ta addabi duniya wato Covid-19 a cewar kafar yada labaran kasar KCNA.

Manufar ziyarar tasa ita ce don sabunta dankantakar kawancen jamhuriyar kasar KTA da Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG