Kungiyoyin raya kasa sun yi taro domin tabbbatar da zaman lafiya a Najeriya, tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan Najeriya bisa la'akari da irin kalaman da wasu 'yan siyasa da basu ji dadin yadda sakamakon zabe ya kasance ba.
Da akwai yiwuwar cewa bayanai na baya-bayan nan a game da tsohon karamin Ministan man Najeriya Timipre Sylva mai murabus su iya sanya kafar ungulu a takarar sa na gwamnan jihar Bayelsa bisa zargin ya yi amfani da takardun shaidar karatu na boge.
‘Yan adawa a Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer sun bayyana damuwa dangane da yadda bangaren rinjaye ke haddasa cikas ga tsarin sulhun dake tsakanin bangarorin siyasar kasar.
Babban bankin Najeriya ya ce yana ci gaba da buga sababbin takarkun kudi, sai dai har yanzu 'yan Najeriya na kokowa da cewa, suna cigaba da fuskantar matala wajen samun takadun kudin.
Gwamnatin kasar ta Birtaniyya ta sanar da wannan matakin ne a cikin wani sako da ta wallafa a shfinta na yanar gizo cikin kundin tsarin aikin lafiya da masu ayyukan jinkai.
Gwamnatin Nijar ta bayyana damuwa a kan yadda matsalar 'yan bindiga ta ki karewa a cikin kasar da kuma yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Kungiyar tarayyar turai ta ayyana shirin bada tallafin makamai wa wasu kasashen Afrika masu fama da matsalolin ta’addanci wadanda suka hada da Jamhuriyar Nijer da Somalia
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci Majalisar Dattawan kasar su amince da wani kudurin dokar kare bayyanai wanda sashin zartarwar gwamnatin Najeriyan ya gabatar a Majalisar.
Shelkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa, bata fuskantar wata barazanar tsaro da zata kai ga kawo sojojin kasashen waje cikin kasar.
Tsohon Ministan harkokin matasa a Najeriya Barrister Solomon Dalong ya bayyana mahimmancin dake akwai ga al'ummar Najeriya mabiya addinin Kirista da Musulunci su zauna lafiya da juna.
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta amince da nada tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya INEC, Farfesa Muhammad Attahiru Jega a matsayin uba ga sabuwar Jami’ar nazarin koyar da aikin malinta ta Kano, wato Sa’adatu Rimi University of Education, Kumbotso.
Bulgariya ta kamala dukkanin shirin tattaunawa mai tsawo da sarkakkiya a game da kafa gwamnatin rikon kwarya bayan da aka aka kamala gudanar da zabe sau 5 cikin shekaru 2 inda aka gaza samun wanda yayi nasara.
Kungiyar gwamnonin Najeriya zata gana da EFCC da ICPC domin nazari cikin tsanaki kan yadda gwamnoni su ke kashe kududaden da gwamnatin tarayya ke ware musu na shawo san satsalolin tsaro
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta soma tuntuba da tattaunawa a fadin kasar, dangane da yiwuwar soke hukuncin kisa kan mutane da aka sama da laifin kisan kai.
Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen ta ce duk wani “matsin lamba daga waje,” ba zai hana tsibirin mai cin gashin kan sa mu’amala da sauran duniya ba.
Hukumar tsaron farin kaya ta Azerbaijan ta fada a yau Laraba cewa, tana gudanar da bincike kan "wani harin ta’addanci”, bayan da aka harbi wani dan majalisar dokoki mai tsattsauran ra’ayin kin jinin Iran, aka kuma yi masa rauni a gidansa.
A yau Laraba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da tsohon shugaban ‘yan sanda Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa.
Al'ummar jihar Neja suna cikin tashin hankali a sakamakon harin da 'yan bindiga suke cigaba da kaiwa yankunan karkara.
Domin Kari