Yinkurin wasu masu niyyar daura auren jinsi ya ci tura bayan da hukumar Hisbah ta bankado shirin.
Kotun har ila yau, ta ba da umarnin kwace masallatansa guda biyu, tare da haramtawa kafofin yada Labarai na jihar Kano sanya wa'azinsa.
Jihar Kano mai dinbin jama'a ta ce cutar kwalara ta bullo amma tuni ta shiga tinkararta.
Hankula sun tashi a birnin Kano na arewacin Najeriya, bayan wata fashewa a Sabon Gari, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane biyar. Tuni dai hukumomi su ka bayyana cewa tunkunyar gas ta 'yan walda ce ta yi bindiga.
A 'yan kwanakin nan, gabanin karatowar zabukan fidda gwani salon siyasar jihar Kano a Najeriya ya sauya salo, tsakanin bangaren gwamna Ganduje da bangaren Malam Ibrahim Shekarau.
A cigaba da sauye sauyen salo don dacewa da zamani da kuma yanayin kasuwa da ake gani a bangaren fina finai mafi girma a arewacin Najeriya, wato Kannywood, hankulan wasu masu shirya fim ya fara komawa ga fina finai masu dogon zango.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta samu nasarar kama wadanda suka yi garkuwa tare da hallaka Hanifa Abubakar mai shekaru biyar da haihuwa da aka sace a shekarar da ta gabata.
Labarin zababben kansila da ya rungumi sana’ar sayar da shayi a Kano, wanda ya ke karfafa gwiwar sauran matasa da kar su rika raina sana’ar yi.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramta amfani da mutum mutumi ga Masu shagunan sayar da kaya da teloli, inda ta ce yin haka ya sabawa addinin musulunci.
Gwamnan Abdullahi Ganduje ya bukaci janye karar da ya shigar kan dan jarida Jaafar Jaafar, na badakalar bidiyon karbar dala da dan jaridar ya wallafa a shafinsa.
Wata makaranta mai zaman kanta mai suna New Oxford Science Academy dake jihar Kano ta ce ta amince da fara karbar kudin yanar gizo crypto currency a matsayin hanyar biyan kudin makranta.
'Yan mata a jihar Kano da ma sauran jihohin arewacin Najeriya na fuskantar matsanaci tsangwama daga bangaren samari dangane da sanya abaya da ta shigo kwanan nan.
Abin al’ajabi ba ya karewa - A jihar Kano dake Arewacin Najeriya, an samu wani mutun da ya ce shekarunsa tara ya na zaman aure da aljana.