Kwararriya a haujin dinka sitturu ‘yar kasar Mozambique, tana samar da tufafi masu jan hankali da sha’awa. Shaazia Adam tana da burin ganin kayayyakin da take samarwa sun ba da gudummuwa ga ci gaban sha’anin dinka sutura da al’adu a Mozambique.
A fim din Shirley, fitacciyar jaruma Regina King ta fito a matsayin mace bakar fata ta farko da aka zaba a Majalisar Dokoki
Yawanci lokacin bazara a Washington D.C. cike yake da ni’imar bishiyoyi da masu furanni kala-kala na ban sha’awa, to amma yanayin wannan shekara ya zo da wani al’amari na ba zata, sakamakon ƙarancin wadannan furannin fiye da yadda ake tsammani wannan na nuni ne kan haɓakar tasirin sauyin yanayi.
Wata babbar kotu a jihar Kano ta ba da belin Murja Kunya kan kudi naira dubu 500, tare kuma da gindaya mata wasu karin sharuda daga fitowa ko wallafa ko wane irin bidiyo a dukan kafafen social media.
Yadda kubutar da daliban Kuriga wanda yazo kwana guda kafin cikar wa’adin da ‘yan bindigan suka gindaya ya haifar da ce-ce-ku-ce a game da yadda aka yi a ka kubutar da su; Matsalar kwararar baki a birnin New York na Amurka ta rubanya har sau uku daga kasashen Yammacin Afirka, da wasu rahotanni
Mai zane-zane dan Turkiyya Refik Anadol na yin "zane-zane" da "sassaken abubuwa" ta amfani da wata manhaja ta musamman don mayar da wasu bayanai wata fasaha.
Dan siyasar Uganda, Kyangulanyi wanda aka fi sani da Bobi Wine ya ce zaben fim dinsa, The People’s President domin takarar lambar yabo, ya taimaka wajen janyo hankalin duniya kan gwagwarmayar da yake yi ta samar da sauyin dimokaradiyya a kasarsa.
Kungiyoyin FUS Rabat da Petro de Luanda sun sami tsallakewa zuwa matakin wasannin ya da kanin wani. Bari mu duba yadda mawaka ciki har da Musa Keys, da Daliwonga da sauransu, suka nishadantar da jama’a kafin soma wasan da hutun rabin lokaci.
Domin Kari