A taron BAL4HER na wannan shekara mahalarta sun yi magana game da haɓaka ƙwarewar jagoranci na ‘ƴan mata, kwarin gwiwa, da mutuntaka ta hanyar wasan ƙwallon kwando.
Bikin baje kolin fasaha na Washington D.C, wato Awesome Con, ya kuma tattara hancin masoya sama da dubu 70, a wani gagarumin bikin baje kolin fina-finai da wasannin kwaikwayo na nishadantarwa har ma da wasannin ‘yar tsana.
Biyo bayan umurnin shugaba Tinubu na gaggauta ceto daliban Kuriga sama da 280, babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya ce sojoji sun dukufa wajen ganin an ceto daliban da kuma hukunta ‘yan bindigan da ke wannan aika-aika, da wasu rahotanni
A bikin karramawa na Academy karo na 96 na wannan shekara an ga jarumai a cikin fita ta kece raini da tufafi iri daban-daban da ke kyalkyali da daukar ido.
An bude gasar League ta kwallon Kwando ta nahiyar Afirka a ranar Assabar, a dandalin wasanni na SunBet da ke birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu, inda kungiyoyi 4 daga nahiyar za su fafata wasanni 22 a kashin farko na gasar da ake kira Kalahari Conference.
A birnin Mogadishu babban birnin kasar Somalia mai fama da rikice-rikice, dattawa kan tattaru a kowace rana a gundumar Bondere, domin gasar harbin kibau. Gasar dai wani sashe ne na al’adun kasar masu dadadden tarihi.
Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya sa mutanen yankin azumi cikin mawuyacin hali, yayin da kuma ake kara samun fargaba musanman a Jerusalem inda masallacin Qudus yake; Gwamnatoci da wasu masu hali a Najeriya na ci gaba da rabawa mutane kayan abinci don rage musu radadin rayuwa, da wasu rahotanni
Domin Kari