Shugaba Barrack Obama ya fito karara ya yi alla wadai da abin da ya kira “ hare haren jiragen sama na rashin imani da Rasha da Syria” ke kaiwa fararen hula a gabashin birnin Aleppo.
Ministan shari’a a Sudan ya musunta maganar da yan gudun hijira a Jabel Marra ta yankin Darfur suka yi na cewa sun shaki iskar wani sanadari mai guba a hannun gwamnatin Sudan din.
Yan gudun hijira a jihar Taraba na ci gaba da kokawa game da halin da suke ciki ayanzu, inda suka nemi da a gaggauta mayar da su yankunansu da suka fito.
Gwamnatin Somalia ta bukaci bayanai daga Amurka a kan farmakin da ta kai ta sama a ranar Laraba a tsakiyar Somalia.
Bayan shafe kimanin mako guda a tsare, Jiya Alhamis wata kotun Majistire dake Katsina ta bada belin sakataren kungiyar Muryar Talaka Kwamarad Bashir Dauda, wanda gwamnatin jihar Katsina ke tuhuma tare da wasu mutane biyu da laifin bata mata suna ta hanyar rubuce-rubuce a kafofin sadarwa na sada zumunci.
A jiya Laraba farashin danyen mai ya tashi, biyo bayan rahottanin da aka bada masu cewa Kungiyar kasashe masu arzikin mai suka cimma matsayar yawan man da suke hakowa.
Majalisar dokokin Amurka ta kawarda wani shirin doka na shugaba Barrack Obama da ya nemi hanawa Amurkawa kai karar Saudiya gaban kotu don neman hakkinsu a dalilin harin ta’addancin ranar sha daya ga watan Satumban shekarar 2001 da aka kawo wa Amurka.
Masu bincike na kasa da kasa sun ce jirgin saman fasinjan nan na Malaysia da ya fadi a gabashin kasar Ukraine a cikin watan Yuli 2014 wani makami mai lizzami ne ya harboshi wanda aka aika zuwa kasar Rasha daga Ukraine.
Dakatar da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai Abdulmumin Jibrin tsawon kwaman kwana 180 na Majalisa, ya jawo masu ganin hakan dai dai ne, da wadanda suke ganin da Majalisar ta jira hukuncin kotu bisa karar da dan Majalisar ya shigar.
Kungiyar Arewa Citizens Action for Change (ACAC) ta matasan Arewa masu rajin kawo sauyi a sha’anin tafiyar da harkokin mulki a Najeriya ta bada wa’adin makonni biyu ga kungiyar Dattawan Arewa ACF da su gudanar da taron masu ruwa da tsaki game da mawuyacin halin da talakawan Arewa ke ciki dama na kasa baki daya domin fadakar da gwamnatin tarayya ta dauki matakin daya kamata.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya jagoranci taron mako – mako da ake yi, na Majalisar Zartarwa ta gwamnatin kasar inda akayi tsokaci da nazari tare da yanke muhimman shawarwari akan samar da ruwan sha da aiki a fadamu da kuma Noma.
A dai dai lokacin da ake ta cece kuce a Najeriya tsakanin gwamnatin kasa da ‘yan kungiyar kwadago da kuma wani bangare na kwararru akan sha’anin tattalin arziki dangane da tasiri ko rashin tasirin Najeriya ta sayar da wasu kamfanoni domin samun kudin shiga.
Karshenta dai an rantsar da shugaba Ali Bongo Ondimba a matsayin shugaban Gabon a karo na biyu na tsawon wani sabon wa’adin mulki na shekaru bakwai bayan ya lashe zaben da aka yi da ‘yan kuri’u kalilan.
A wannan babban hukuncin da ba’a taba yanke irinsa ba, kotun kasa da kasa ta duniya a jiya Talata ta yankewa wani mutum mai tsaurin ra’ayin musulunci hukunci bayanda ta same shi da laifin nakkasa wasu kayan tarihi masu muhimmanci a kasar Mali.
Masu aikin ceto a Egypt a jiya Talata sun tsamo gawarwaki bakin haure da dama da suka nitse a cikin jirgin ruwar masunta a gabar tekun Mediterranean wanda ya kai a dadin wadanda suka mutu sama da dari biyu a hadarin jirgin ruwa da ya faru ran 21 ga watan nan na Satumba.
Tsohon shugaban Isra’ila kuma tsohon frayim-ministanta Shimon Peres, wanda ake cewa ya share tsawon duk shekarun kafa Isra’ila yana bauta mata, ya rasu, yana da shekaru 93 a duniya.
A yau dai ake sa ran kwamitin Ladabtarwa na Majalisar Wakilan Najeriya zai gabatar da rahotansa kan tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar, Abdulmumin Jibrin, wanda yaki bayyana gaban kwamitin.
Masana a harkar masana’antu sun bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki almundahana da makarkashiya da wasu jami’an gwamnati ke yi wajen durkusar da masana’antun Najeriya da sunan zawarcin masu saka jari daga kasashen ketare.
A wani sabon yunkuri na magance matsalar fyade da kuma ‘yan jagaliya, sarakunan gargajiya a jihar Adamawa dake Arewa maso Gabashin Najeriya, sun fara kafa dokar hana tallace tallace da yan mata ke yi.
Domin Kari