Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarakunan Gargajiya Sun Fara Kafa Dokar Hana Yan Mata Tallace Tallace


Wasu yan mata dake talla

A wani sabon yunkuri na magance matsalar fyade da kuma ‘yan jagaliya, sarakunan gargajiya a jihar Adamawa dake Arewa maso Gabashin Najeriya, sun fara kafa dokar hana tallace tallace da yan mata ke yi.

Kafa dokar kuwa ya biyo bayan bullar wata kungiyar da akewa lakabi da ‘Yan Shila, dake karbe kudade da wayoyin hannu da jakankuna daga hannun ‘yan mata suna yi musu fyade.

‘Dan Isan Adamawa hakimin Jimeta dake fadar jihar, Alhaji Inuwa Baba, wanda a yankinsa ne lamarin yafi kamari, yace sun dauki wannan mataki ne sakamakon irin barnar da matasa ke yi a yanzu, na baya bayan nan ma shine wani fyade da wasu matasa suka yiwa wata yarinya har ta rasa ranta.

A lokacin da wasu mutanen yankin ke maraba da dokar wasu kuma ganin a cikin yanayin da ake ciki yayi matsi sosai, domin wasu yaran su ke taimakawa iyayensu.

Sai dai kuma rundunan ‘Yan Sandan jihar tace zata sa kafar wando guda da duk wanda aka kama yana aikata ba wannan tu’annatin.

Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG