Biyo bayan kazafin da Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako mai ritaya yayi wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na yunkurin yiwa jama’ar arewacin Najeriya kisan kare dangi, jama’a da dama da kungiyoyi da shuwagabanni na mayar da martani, wasu suna yaba mishi, wasu kuma suna sukarshi.