Accessibility links

Hassan Sheikh Mohamud Ya Zamo Shugaban Somaliya


Wani sojan gwamnatin Somaliya yana wucewa a kusa da wata mace rike da kwalin fasta na yakin neman zaben shugaba Sheikh Sharif Ahmed

Wannan sabon shiga a siyasa ya doke shugaba mai ci, Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, a zagaye na uku na zaben shugaban kasa sabo a majalisar dokoki

Wani dan takarar da ba kowa ne ya san shi ba ya lashe zaben shugaban kasar Somaliya, a bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'a a zagaye na uku na zaben shugaban kasar karkashin wani shirin da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya.

Hassan Sheikh Mohamud mai shekaru 56 da haihuwa, ya doke shugaban kasar Somaliya mai ci, Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, inda ya samu kuri'u fiye da 150 daga cikin kuri'u 271 da 'yan majalisar dokoki suka jefa.

Babu wanda ya samu kashi biyu bisa uku na kuri'u a zagayen farko, saboda haka 'yan takara hudu da suka fi samun kuri'u suka je ga zagaye na biyu. A zagaye na biyun kuma, babu wanda ya samu fiye da rabin kuri'un 'yan majalisar dokokin, saboda haka shugaba mai ci Sheikh Ahmed da shi hassan Sheikh Mohamud suka shiga zagaye na uku.

Shi dai sabon shugaban na Somaliya, shi ne ya kafa jam'iyyar nan ta Zaman Lafiya da Raya Kasa (Peace and Development Party) ko kuma PDP a takaice. Shi dan rajin kyautata rayuwar jama'a ne, kuma sunansa ya fito sosai cikin 'yan takarar a bayan da ya samu kuri'un mutanen da ba su gamsu da shugabannin kasar na yanzu ba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG