Accessibility links

Kasashe Uku Sun Kara Shiga Shirin Tabbatar da Wadatar Abinci Na Afirka

  • Ibrahim Garba

Shugabannin kasashen cikin kungiyar Tarayyar Afirka a wurin taron
Kasashen Burkina Faso, da Ivory Coast da Mozambique sun shiga wani shirin kasa da kasa na tabbatar da wadatar abinci da kuma magance matsalar karancin abinci a Afirka.

Kasashen sun shiga cikin wani Sabon Gayyama ta Tabbatar da Wanzuwar Abinci da Ingancinsa da kungiyar manyan kasashe 8 ta kaddamar a farkon wannan shekarar.

Tsarinsu ya hada da hulda da manyan kamfanonin kasa da kasa da kamfanonin Afirka, da zummar ceto muta wajen miliyan 50 a Afirka yamma da Sahara daga talauci cikin shekaru 10 masu zuwa.

Jami’an gwamnatin Amurka sun bayar da sanarwar kafa kungiyar a jiya Laraba. Sabbin mambobin sun hadu da Habasha, da Ghana da Tanzania wadanda tun cikin watan Mayu su ka shiga wannan shirin.

Kasashen sun yi alkawarin gudanar da sauye-sauye, ciki har da kari a kudaden da su ke kashewa kan harkokin noma, da ingantawa da kuma ni’imta gonaki, da tayar da komadar mata da iyali, da kuma sauye-sauye a fannin abubuwan da suke fitarwa kasashen waje da kuma haraji wadanda ke kashe jikin ‘yan kasashen waje masu saka jari a fannin aikin noma.
XS
SM
MD
LG