Accessibility links

Sabuwar Shugabar AU na Mali Gabanin Taron Neman Mafita

  • Ibrahim Garba

Sabuwar Shugabar Kungiyar AU Nkosazana C. Dlamini-Zuma

Sabuwar Shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka ta isa kasar Mali don halartar wani taron kasa da kasa

Sabuwar Shugabar Kungiyar Tarayyar Afirka ta isa kasar Mali don halartar wani taron kasa da kasa da ake yi na nemo hanyoyin kawo karshen dambarwar soji da na siyasa a kasar.

Wakilan kungiyoyin Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da na ECOWAS za su tattauna kan hanyoyin dawo da dimokaradiyya a Mali da kuma yadda za a bullo wa ‘yan bindigar Islama da ke arewacin kasar a taron da za a yi a gobe jimma’a a birnin Bamako.

Shugabar ta kungiyar Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini Zuma ta ce al’amarin na Mali wani rikici ne da tasirinsa ya zarce yankin kuma ya na iya yaduwa zuwa dukkannin sauran sassan Yammacin Afirka muddan ba a shawo kansa ba.

Ana sa ran wakilan za su tattauna game da lokacin da ya dace sojojin kungiyar ECOWAS su kai dauki, wadda it ace kungiyar kasashen yammacin Afirka.

A makon jiya Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga AU da ECOWAS da su gabatar da tsare-tsaren kai dauki cikin kwanaki 45.

Kwamitin na bukatar sake kada kuri’a game da ko za ta amince da kai daukin ko kuma za ta bukaci a sake garanbawul ga shirin.

A halin da ake ciki kuma daruruwan ‘yan Mali sun fito kan titunan Bamako don yin zanga-zanga kan shirin kai daukin sojojin kasashen waje.

Kasar ta Mali dai ta shiga rudu ne sanadiyyar juyin mulkin ran 22 ga watan Maris da ya hambarar da gwamnatin shugaba Amadou Toumani Toure.

Jerin kungiyoyin ‘yan kishin Islama ciki har da reshen al-Qaida na Arewacin Afirka sais u ka kwace ikon da yankin Hamada na arewacin kasar, kuma a yanzu su ke da iko da kashi biyu bisa ukun fadin kasar ta Mali.
XS
SM
MD
LG