Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zarginsu Da Yunkurin Kashe Shugaba Boni Yayi


Shugaba Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin yana jawabi gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya

An kama Zouberath Kora, 'yar'uwar shugaban na Jamhuriyar Benin da likitansa da wani tsohon ministansa bisa zargin sun yi kokarin ba shi guba.

An kama wata ‘yar’uwar shugaba Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin, tare da likitansa da kuma wani tsohon minista, ana tuhumarsu da kulla makarkashiyar maye gurbin wani maganin da yake sha da guba.

Mai gabatar da kararraki yace an kama ita wannan ‘yar’uwar shugaban, da likitansa da kuma tsohon ministan harkokin kasuwanci, Moudjaidou Soumanou, ana tuhumarsu da laifuffukan yunkurin kisan kai, da kulla makarkashiya a saboda rawar da ake zargin sun taka a wannan lamarin.

Masu gabatar suka ce an yi tayin bayarda ladar kusan dala miliyan 2 ga ita wannan ‘yar’uwar shugaba Boni Yayi mai suna Zouberath Kora, da likitansa Ibrahim Mama Cisse domin su maye gurbin wani maganin da shugaban yake sha da wata gubar da zata yi masa lahani a lokacin da yake ziyara a birnin Brussels a cikin wannan wata.

Masu gudanar da bincike suka ce asirin mutanen ya tonu a bayanda ita wannan ‘yar’uwa ta shugaban ta fada ma wata ‘yar’uwarta dabam irin abinda suek kullawa.

Masu gabatar da kararraki suka ce su na kyautata zaton cewa wani dan kasuwa mai suna Patrice Talon wanda suka bata kwanakin baya da shugaban kasar, shi ne ya kitsa wannan makarkashiya ta kashe shugaban da guba. Hukumomi su na neman Talon, wanda ba ya kasar a yanzu.
XS
SM
MD
LG