Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Ayyana Shiga Bala'i A Jihar New York


'Yan kwana-kwana a New York su na amfani da kwale-kwalen roba a kan babban titin nan na 14th St domin ceto mutane daga gidajensu

Sa'o'i kadan a bayan da Sandy ta haddasa mummunar ambaliya, da gobara, da mace-mace da kuma dauke wutar lantarki ga miliyoyin jama'a a birnin da ya fi girma a duniya.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya ayyana shiga cikin yanayi na bala'i a Jihar New York, 'yan sa'o'i kadan a bayan da gagarumin hadarin ruwan teku mai tattare da guguwa da aka sanya ma suna "Sandy" ya ratsa ta kan gundumar Manhattan, ya haddasa ambaliyar ruwa kan titunan dake kwari tare da dauke wutar lantarki a akasarin fadin birnin New York.

Wannan ayyanawa ta yau talata, tana nufin za a ware kudaden agaji na gwamnatin tarayya domin taimakawa Jihar wajen ayyukan jinkai ga wadanda suka tagayyara.

Wannan hadari da guguwa da suka hauro kan doron kasa daga teku a kudu da birnin New York, yanzu tsananinsu ya ragu a yayin da suke bi ta kan doron kasa. Amma kuma har yanzu Sandy tana tattare da guguwa mai juyawar kimanin kilomita 100 cikin sa'a daya. Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa ta Amurka ta ce ana sa ran wannan hadari da guguwa zasu tsallaka cikin kasar Canada ya zuwa gobe laraba.

Hadarin ruwan na teku ya juye ruwan sama mai tsananin yawa, da iska mai karfin gaske da kuma igiyoyin ruwa masu girma da karfi daga tekun Atlnatika zuwa bakin gabar gabashin Amurka, inda ya fi ko ina cunkoson jama'a. Mutane akalla 14 suka mutu a yankin gabashin Amurka a sanadin wannan hadari da guguwa, akasari a hadarurrukan motoci ko kuma yayin da bishiyoyi ke fadowa kan gidajensu.

Gundumar Manhattan a birnin New York, ta fuskanci ambaliyar ruwan da ya kai na mita 4, abinda ya sa komai ya tsaya cik a wannan cibiyar hada-hada ta birnin New York. Mutane fiye da miliyan daya suka rasa wutar lantarki a wannan birni da ya fi ko ina yawan jama'a a nan Amurka. Gidaje da kamfanoni fiye da miliyan 6 sun rasa wutar lantarki a fadin bakin gabar gabashin Amurka da wasu wuraren dake can cikin doron kasa, ciki har da nan Washington da jihohin dake makwabtaka da ita.

A cikin New York, titunan karkashin kasa da na jiragen karkashin kasa duk sun cike da ruwa, ciki har da inda ake sake gini a Hasumiyar Cibiyar Cinikayya ta Duniya. An umurci mutane da dama da su bar gidajensu. A wata unguwa mai suna Chelsea, gefe guda na wasu jerin gidaje ya rushe, inda aka bar dakunan mutane da kayan cikinsa a waje. An ga ruwan ambaliya ya dauko motoci dama yana tafiya da su a kan titunan unguwannin da ba su kan tudu a birnin.

Al'amura sun tsaya cik a wasu biranen dake gabashin Amurka, ciki har da nan birnin Washington a Gundumar Columbia, inda a rana ta biyu a jere aka soke zirga-zirgar jiragen kasa da motocin safa, aka rufe filayen jiragen sama, sannan aka ce miliyoyin jama'a su yi zamansu a gida ba aiki. A wuraren da suke kan tuddai da duwatsu kuma, ruwan dake tattare da wannan guguwa ya ci karo da iska mai tsananin sanyi ya zamo dusar kankara mai yawan gaske. An yi hasashen cewa yawan dusar kankarar da zata sauka a wasu wuraren zata kai tsawon mita guda.

Wannan hadarin ruwa da guguwar teku mai suna Sandy dai, fadinta ya kai kilomita dubu daya da dari biyar.

Hukumomi a jihohi 9 da kuma cikin Gundumar Columbia sun ayyana kafa dokar-ta-baci. An rufe dukkan ofisoshin gwamnatin tarayya jiya litinin, kuma za a ci gaba da rufe su duk tsawon yau talata. Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce an sanya dogarawan tsaron cikin gida har dubu 2 su taimaka wajen ayyukan agaji, yayin da aka ce ma wasu dubu 60 su zauna cikin shiri ko da za a bukace su.

Jiragen helkwafta na dogarawan tsaron bakin tekun Amurka sun ceto ma'aikata 14 na wani jirgin ruwa mai suna HMS Bounty wanda ya fara nutsewa a dab da gabar Jihar Carolina ta Arewa. Daya daga cikin ma'aikatan ya mutu daga baya a asibiti. Rundunar tsaron gabobin tekun ta ce daga baya jirgin ruwan ya nutse.

Sandy ta kashe mutane akalla 65 makon jiya a yankin tekun Carribean, kafin ta doso nan Amurka.
XS
SM
MD
LG