Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Amurka


Mitt Romney (l) and President Barack Obama
Fafatawa mai zafi, wadda kuma aka dau lokaci mai tsawo ana yi, ta neman zama Shugaban Amurka na shekaru hudu daga yanzu, ta zo karshe a yayin da ‘yan takarar biyu da kowannensu ke da tasiri, ke ta ziyarce-ziyarcen jihohi da dama a yinkurinsu na karshe na karya lagwan kankankan din da aka yi, kamar yadda kuri’ar jin ra’ayin jama’a ke nunawa.

Kalilan ne kawai daga cikin jihohi 50 na kasar ake masu ganin fagagen daga, musamman ma irinsu Ohio da Florida da Wisconsin da Virginia da kuma Iowa. Karamar jihar nan ta Hampshire ma ta shiga sahun wadannan jihohi shida din da ake ganin cikin ‘yan takarar biyu babu mai galaba gabanin zaben na gobe Talaba.

Yau Litini, Shugaba mai ci Barack Obama ya koma Wisconsin, Iowa da Ohio don gudanar da gangamin yakin neman zabe, kafin ya doshi garin haihuwarsa Illinois na jihar Chicago inda zai kasance zuwa daren zaben.

Abubuwan da mai kalubalantarsa na jam’iyyar Republican, Mitt Romney, zai yi yau Litini, sun hada da yada zango a Florida da safe kafin ya koma Virginia, da Ohio da kuma New Hampshire. Da daren zabe zai kasance a birnin Boston da ke jiharsa ta haihuwa ta Massachusetts.

Dukkannin ‘yan takarar biyu sun yi ta bayyana gaban cincirindon jama’a masu cike da kuwa a jiya Lahadi a yayain yada zango da su ka yi ta yi a muhimman jihohi.
XS
SM
MD
LG