Accessibility links

Obama ya ci jihar Florida, don haka ya dada tsere ma Romney a adadin kuri'u na karshe

  • Ibrahim Garba

U.S. President Barack Obama delivers a statement on the U.S. "Fiscal Cliff" in the East Room of the White House, November 9, 2012.
An bayyana Shugaban Amurka Barack Obama a matsayin wanda ya ci zaben jihar Florida inda aka fi yin kare-jini biri-jini, kwanaki hudu bayan da ya sake yin nasara a zaben Shugaban kasa.

Jihar ta Florida da ke kudancin kasar, ita ce kawai jihar da ta kasa kammala kidaya kuri’unta bayan zaben na ranar Talata, wanda Shugaba mai ci dan Democrat da dan Republican Mitt Romney su ka fafata a ciki.

Ofishin harkokin cudanyar na jihar Florida y ace Shugaba Obama ya sami kashi 50% na kuri’un da aka kada a yayin da kuma Romney ya sami kashi 49.1 %, mai nufin tazarar kuri’u 74,000, wanda ya kai adadin da ya wace wanda akan sake kirgawa.

Ko da ma baici jihar da ake wa kirari da “mai hasken rana” tuni ba Shugaba Obama ya sami sama da makin kuri’u 270 da ake bukata kafin zama Shugaban kasa.

A Amurka dai kowace jiha na da adadin makin kuri’u daidai gwargwadon yawan mutanen cikinta, kuma yawan makin na zama daidai da yawan ‘yan Majalisar Dattawanta da na Wakilanta. Duk dan takarar da ya sami kuri’u mafi yawa a jiha, to shi ya ci makin kuri’un jihar, in banda jihohin Maine da Nebraska.

Karin makin kuri’un Florida 29, ya sa adadin makin kuri’un Mr. Obama ya kai 332 na Romney kuma 206.
XS
SM
MD
LG