Accessibility links

An Kafa Takunkumi Kan 'Yan Tawayen M23 Na Kwango


Mutane su na gudu daga garin Goma a yayin da 'yan tawayen M23 ke arangama da sojojin gwamnati

Dukkan wakilan Kwamitin Sulhun sun amince da kudurin kafa takunkumin tare da yin Allah wadarai da tallafin da wasu kasashen waje ke ba 'yan M23

Dukkan wakilan Kwamitin Sulhun MDD sun jefa kuri’ar amincewa da kudurin kafa takunkumi a kan shugabannin kungiyar ‘yan tawayen M23 ta kasar Kwango-ta-Kinshasa.

Har ila yau, wannan kudurin da kasar Faransa ta gabatar ya bukaci ‘yan tawayen da su janye nan take daga muhimmin birnin Goma dake kan iyakar Kwango da Rwanda, sannan yayi Allah wadarai da goyon bayan da wasu kasashen waje ke ba ‘yan tawayen na Kwango.

Kwamitin Sulhun ya jefa kuri’ar ce talata da maraice, sa’o’i a bayan da dakarun 'yan tawaye na kungiyar M23 suka kwace wannan birni na Goma dake bakin iyaka da Rwanda ba tare da turjiya ba. Sojojin gwamnatin Kwango sun gudu, yayin da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya su dubu daya da dari biyar suka tsaya kawai su na kallo.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, yace abin kunya ne a ce akwai sojojin kiyaye zaman lafiya su dubu 17 a cikin kasar Kwango, amma sun kasa hana wasu 'yan daruruwan mutane kwace wannan birni.

Amurka ta yi kiran da a gudanar da tattaunawa a tsakanin Kwango da makwabtanta Rwanda da Uganda.

Kwango ta Kinshasa ta ce ba zata tattauna kai tsaye da kungiyar M23 ba sai idan an hada da kasar Rwanda a ciki. Shugaba Joseph Kabila na Kwango yana zargin Rwanda da laifin goyon bayan 'yan tawayen, zargin da wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ma ya gaskata shi. Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya musanta wannan zargin.
XS
SM
MD
LG