Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Aikata Cin Zarafin Bil Adama.


'Yan kungiyar Boko Haram ta Najeriya wadda Kotun Duniya ke zargi da aikata manyan laifuffukan cin zarafin Bil Adama

Babbar Lauyar Kotun Duniya mai shigar da kara Fatou Bensouda ta zargi Boko Haram da kisan kai da gallazawa.

Babbar lauyar kotun duniya mai shigar da kara ta zargi ‘yan tawayen Boko Haram da aikata manyan laifuffukan cin zarafin bil Adama a Najeriya, musamman ma kisan kai da tsangwama.

Ofishin babbar lauya Fatou Bensouda ya ce akwai kyakkyawar madogarar da ta tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ta tsara wani gagarumin harin gama gari wanda ya yi sanadiyar mutuwar Kiristoci da Musulmi fiye da dubu daya da dari biyu daga wajejen tsakiyar shekarar dubu biyu da tara.

Rahoton, wanda aka kwarmatawa kafofin yada labarai, ya bukaci hukumomin Najeriya da su gurfanar da wadannan manyan laifuffuka a gaban kotu, in ba haka ba, kotun duniya za ta iya daukan matakin yin hakan ita da kan ta.

Game kuma da zarge-zargen cewa cibiyoyin jami’an tsaron Najeriya su ma, su na aikata laifuffukan cin zarafin bil Adama, rahoton ya ce babu wata alamar da ta nuna cewa, wadannan abubuwan da ake zargin su da aikatawa na daga cikin wata manufar gwamnati ko tsarin da aka shirya takanas da sunan cin mutuncin fararen hula.

A watan jiya, kungiyar kare hakkokin bil Adama ta Human Rights Watch, ta ce daga shekarar dubu biyu da tara fadan da ake yi tsakanin Boko Haram da gwamnatin Najeriya ya lankwame rayukan mutane fiye da dubu biyu da dari takwas, daga cikin su kamar dubu daya da dari uku sun mutu ne sanadiyar irin matakan da jami’an tsaron Najeriya ke dauka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG